Jerin Mutanen Da Baza Su Biya Sabon Kudin Harajin Bankuna Da Gwabanati Ba
![]() |
Su wane ne ba za su biya sabon harajin CBN ba? |
A ranar Litinin ne Babban bankin Najeriya, CBN ya sanar da bijiro da tsarin cirar kashi 0.5 cikin ɗari a duk lokacin da aka tura kuɗi ta asusun banki da za a yi amfani da su wajen tabbatar da tsaro ta intanet.
Duk da cewa CBN ya bijiro da harajin da ya janyo cece-ku-ce, bankin ya yi bayani cewa akwai waɗanda tsarin bai shafe su ba.
Jerin waɗanda harajin bai shafa ba
Kuɗin bashi: Bayarwa da kuma biyan bashi
Kuɗin albashi
Tura kuɗi tsakanin asusu da asusu a banki guda ko tsakanin banki da banki ga abokin hulɗa ɗaya.
Tura kuɗi daga wani asusu zuwa wani tsakanin abokan hulɗar banki ɗaya
Umarnin cibiyoyin hada-hadar kuɗi ga wasu bankunan
Kuɗin da bankuna ke tura wa CBN da kuma wanda babban bankin ke tura wa bankuna
Tura kuɗi tsakanin ressan bankuna a cikin banki ɗaya
Hada-hadar kuɗi tsakanin bankuna da aika kuɗi tsakanin bankin mai karɓa da kuma tura kuɗi da kuma ajiyar bankunansu.
Takardar tabbatar da tura kuɗi
Ajiya da tura kuɗi har da hada-hadar da ta shafi hannun jari na dogon zango kamar treasury bills da takardun lamuni da takardun alƙawarin biyan ƙayyadadden kuɗin ruwa
Shirye-shiryen gwamnati na inganta walwalar jama’a kamar biyan kuɗin fansho
Hada-hadar kuɗi don taimako har da tallafi ga cibiyoyin da ba na neman riba ba masu rajista
Hada-hadar kuɗi na cibiyoyin ilimi har da biyan kuɗin makaranta da sauran hada-hadar da ta shafi makarantu da jami’oi da sauran cibiyoyin ilimi.
Hada-hadar kuɗi a asusun banki na cikin gida kamar asusun wucen gadi na suspense account da clearing account da asusun kamfani na tattara riba da asara da hada-hada a reshen banki da ka iya haɗawa da asusun da ake kula da su a wani reshen bankin da asusun ajiya domin yin tattali da asusun ajiya da bankuna ke buɗewa a wasu bankunan da asusun da ɓangarori ke ajiye kuɗi domin yin cinikayya.
SERAP ta buƙaci a soke harajin
Ƙungiyar ƙoƙarin tabbatar da adalci ta SERAP ta nuna adawarta da sabon harajin na tsaron intanet.
Ƙungiyar ta buƙaci shugaban Najeriya Bola Tinubu da ya bai wa Babban Bankin Najeriya umarnin soke harajin kasancewar ya saɓa wa kundin tsarin mulkin Najeriya da kuma walwalar al’umma.
Wannan haraji zai zamo ɗoriya ne a kan jerin haraje-haraje da al’ummar Najeriya ke biya waɗanda Babban bankin ƙasar ya ƙaƙaba.
Cikin su akwai harajin kula da katin ATM, da kula da asusun ajiya, harajin gwamnati, cajin tura kuɗi daga wani banki zuwa wani da kuma harajin tura kuɗi ta laturoni.
Leave a Reply