Majalisar wakilan Najeriya ta umarci CBN ya dakatar da harajin tsaron intanet

 

Mambobin majalisar wakilan Najeriya sun umarci babban bankin ƙasar, CBN ya janye aiwatar da harajin tsaro na intanet da zai cire kashi 0.5 cikin ɗari a duk lokacin da aka tura kuɗi ta asusun banki.

‘Yan majalisar sun bayyana matakin a matsayin abu mai sarƙaƙiya.

Wannan buƙatar dai na zuwa ne a matsayin martani ga wani kuduri kan bukatar gaggawa na dakatar da gyara aiwatar da harajin tsaron intanet, wanda Kingsley Chinda ya gabatar.

A cewar ƴan majalisar, CBN ya janye takardar aiwatar da tsarin da ya fitar , sannan kuma ya fayyace tsarin yadda ‘yan Najeriya za su fahimta.

Majalisar ta kuma nuna damuwa kan cewa za a aiwatar da dokar cikin kuskure idan ba a dauki matakin gaggawa ba, don magance matsalolin da ke tattare da fassarar umarnin na CBN da kuma dokar tsaro ta Intanet.

A ranar 6 ga watan Mayun shekarar 2024 ne babban bankin kasar CBN, ya fitar da wata sanarwa da ta umarci dukkan bankun da masu gudanar da hada-hadar kudi ta wayar salula su aiwatar da wani sabon harajin tsaro ta intanet saboda hana aikata laifuka ta intanet.


Published on: May 9, 2024. at: 3:38 pm

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*