Menene "rai" a mahangan kimiyya, musamman a ilimin biology?

Menene “rai” a mahangan kimiyya, musamman a ilimin biology?

Da farko dai shi ‘soul’ idan za’a fassarashi da “rai” toh al’amari ne dake da alaqa da falsafa da kuma addinai sabida bayada mazauni a kimiyya shiyasa kimiyya bata duƙufa wajan ganoshi ba, asali ma abu ne da yake kamada al’mara ko camfi idan zamu aunashi da ilimin biology.
Idan kuma rai shine yake sa halitta yayi motsi, ya girma, ya haɓaka kuma yayi numfashi, zamu iya cewa kenan rai gadonta ake daga iyaye (it’s genetic )
Idan kuma rai abune mai zaman kansa (independent entity) dake ɓoye cikin gangan jikin halitta, zamu iya cewa rai wani al’amari ne dake kama da camfi wanda baida asali a ilimin kimiyya.
Mu koma ilimin biology…
Me yake sa halitta yayi motsi, ya cigaba da girma kuma ya haɓaka? sannan me yake sa halittan ya daina motsi, ya daina numfashi idan ya mutu?
(1) Idan rai shine abunda yake ‘motsi’ kuma yake ‘girma’ kuma yake haɓaka/haihuwa to tushen abu mai rai shine ɗigon halitta wanda akafi sani da “cell”
Wato duk wani halitta da ka sani, kamo daga bishiya,mutum, dabba, da sauransu, kwayoyin halittan cell ne suka haɗe da juna suka samardashi, sannan kowanne ƙwayan halittan (ko ɗigon halitta) yanada rai (saboda cell yana haihuwa/replicating)
wato duk wani halittan da kake gani rayuka ne daban daban suka haɗe suka samarda babban rai guda ɗaya, lokacin kwayoyin halittan nan suka mace gabaki ɗaya, shine za’ace halittan ta mace/mutu a hukumance.
(2) Ka ɗauki misali da kadangare, lokacinda jelen kadankare ya rabu da gangan jikinsa, zakaga gangan jikin da wutsiyan duk suna motsi, daga karshe sai ‘cells’ da suke haɗe da jelen/wutsiyan su mace gabaki ɗaya, gangan jikin kuma yaci gaba da rayuwa, dalilin da yasa gangan jikin zai ci gaba da rayuwa shine: na farko acan ƙwakwalwa yake, sabida ƙwakwalwa shi yake turawa gaɓɓan jiki da sakonni, na biyu, sabida acan manƴan sassan jiki suke, kamo daga hanta, koda, zucuya, idanu, da sauransu.
Da’ace ‘rai’ independent entity ne da lokacinda wutsiyan kadangaren ya rabu da gangan jikin, toh wutsiyan ba zaiyi motsi ba na sawon wani lokaci koma bayan yadda muke gani.
Wato yadda kaga mota yake bukatan duk sannan jikinsa (parts) kafin ya fara motsi (movement ) haka halitta yake bukatan sassan jiki (tissues and organs) daban daban kafin yayi rayuwa ko ya zama rayayye (living organism), babu wani abu guda ɗaya da yake sa mota yayi motsi, haka kuma halitta.
A rubutun mu ga gaba, zamu kawo muku cikakke bayani akan abinda muke kira ‘rai’ a rashin sani, da kuma dalilai dake nuna gadonsa ake, harma da tarihinsa.
Muna maraba da duk wani ‘comment’ da za’a ginashi a kimiyyance kaman yadda rubutun mu ya karkata akan ilimin kimiyya zalla, muna godiya.


Published on: May 2, 2024. at: 4:38 pm

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*