United za ta dauki Southgate madadin Ten Hag, ana ta rububin Greenwood

 United za ta dauki Southgate madadin Ten Hag, ana ta rububin Greenwood

United za ta dauki Southgate madadin Ten Hag, ana ta rububin Greenwood

Aston Villa tana da tabbacin za ta sha gaban Arsenal da Manchester United wajen rige-rigen sayen ɗan kwallon Faransa, Michael Olise, mai shekara 22 daga Crystal Palace. (Football Transfers)

Tottenham ta shirya bai wa Ange Postecoglou makudan kudi a badi, domin ya saye ƴan wasan da ke cin kwallo da kuma masu buga tsakiya. (Times – subscription required)

A kalla kungiyoyin Premier League biyu ne ke fatan sayen Mason Greenwood, mai shekara 22, amma watakila ɗan wasan Manchester United a sayar da shi ga kungiyar waje, wanda ke wasannin aro a Getafe ta Sifaniya. (Telegraph)

Manchester City da dan ɗan kwallon tawagar Portugal, Bernardo Silva, mai shekara 29, na son a fayyace masa makomarsa kafin zuwa gasar Euro 2024 a bana a Jamus. (Mirror)

Chelsea ta kulla yarjejeniyar baka-da-bak da Palmeiras, kan daukar matashin Brazil, mai shekara 17, Willian Estevao. (Fabrizio Romano)

Manchester United ba za ta dauki madadin Erik ten Hag ba kan yawan daukar kofi da kocin ya yi kadai, hakan ake sa ran kociyan Ingila, Gareth Southgate yana da damar maye gurbin ɗan kasar Netherlands a Old Trafford. (Telegraph)

Akwai batun cewar an tuntubi juna tsakanin Manchester United da Bayern Munich kan cewar Thomas Tuchel ya koma horar da tamaula a Old Trafford. (talkSPORT)

Ɗan kwallon Borussia Dortmund, mai shekara 34, Marco Reus, wanda yarjejeniyarsa za ta kare a karshen kakar nan na tattaunawa da kungiyar da ke buga Major League Soccer ta Amurka, St Louis City kan batun komawa can da taka leda. (Athletic – subscription required)

Ɗan kwallon tawagar Denmark, Martin Braithwaite zai bar Espanyol a matakin mara kwantiragi a watan Yuli, idan kungiyar ta samu gurbin shiga gasa ta gaba, idan hakan bai yiwuba zai iya barin kungiyar kan Yuro 600,000 euros. (Fabrizio Romano)

Galatasaray na daf da sayen ɗan wasan Chelsea, Hakim Ziyech, bayan da ya taka rawar gani a wasannin aro da ya yi wa kungiyar Turkiya a kakar nan. (Standard)

West Ham za ta fuskanci kalubale daga kungiyar Serie A, Napoli a kokarin da take na shirin sayen dan wasan Anderlecht ɗan kasar Belgium, Zeno Debast. (AreaNapoli via Sport Witness)

Ana alakanta tsohon kociyan Hamburg, Tim Walter a matakin wanda zai maye gurbin Liam Rosenior a Hull City mai buga Championship . (Sky Sports)


Published on: May 9, 2024. at: 8:51 am

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*