WANI HATSABIBIN MADATSI (HACKER) YA ƘIRƘIRO WATA FASAHAR AI DON GUDANAR DA AYYUKAN ƁARNA
Ɗaya daga cikin abun da ake gudu a duniyar tech yana shirin faruwa, a yanzu haka wani hatsabibin madatsi ya ƙirƙiro wani AI chatbot kawai saboda gudanar da ayyukan kutse.
Saɓanin ChatGPT wanda aka yi masa training da ɗabi’u kyawawa da gujewa ayyukan ɓarna, shi wannan sabon aikin shaiɗancin mai suna WormGPT an samar da shi specifically don gudanar da ayyukan ɓarna.
An sanya wa WormGPT zunzurutin mugunta da miyagun halaye, don babban dalilin da ya sa aka ƙirƙire shi shi ne taimaka wa mugaye wajen gudanar da ayyukansu na ɓarnace-ɓarnace, ta’addanci da sauran miyagun ayyuka a duniyar fasaha.
Wannan aikin wani hatsabibin madatsi ne wanda har yanzu duniya ba ta gane ko wane ne ba.
AI ya fara shiga hannun mugaye, lamarin akwai matsala.
—Muhammad Auwal Ahmad (#Mohiddeen)
Leave a Reply