WASU BORROWING COURSES DA DALILAN DA YASA AKE KOYAR DASU A COMPUTER SCIENCE
Yana daga cikin halin dalibai tuhumar meyasa ko ince menene amfanin wasu courses na borrowing da ake koyar dasu alhali su sunje karatun kimiyyar na’ura mai ƙwaƙwalwa ne wato Computer Science yau zan zayyono wasu dalilai da amfanin wasu courses dinda ake koyarda dalibai wanda ba na Department ba
1. Linear Algebra: Linear Algebra indai ka karanci computer Science abune mai wahala baka yishi ba wasu ma har I da II sukeyi. Acikin wasu darussa da akeyi a Linear Algebra irinsu Mapping, Vector, Coordinate dasu Linear Space da sauransu duk akwai amfaninsu babnar manufar wannan darassan sune ka fahimci ina rumbun ajiye bayanai (Database) yasamo asali, ya tsarin KeyValue Pair yake sannan a ina akasamo ilmin Array, Dictionary da sauransu wadannan sune manufar koyar dakai Linear Algebra. Misali: Map kusan dukkan manyan Programming Languages muke dasu yanzu suna da wannnan tsarin na Mapping, Coordinate kuwa anaso kasan X and Y, X dai dai yake da “Width” a screen din Computer kuma Y dai dai yake da “Height” na screen dun Computer. Idan Muka dauki Vector kuwa zamu iya cewa shima Array ne.
2. Mathematical Method: wannan course din anaso ka fahimci tsarin “Functions” ne wanda kusan kowane Programming Language yana dashi sannan kuma ma yanzu muna functional Programming Languages irinsu Haskell, Clojure da sauransu. Babba dadin dadawa kaga AI (Artificial Intelligence)? Cen yasamo asali shiyasa akeso nanma ka fahimta.
3. Entrepreneurship: Anaso kakoyi yadda zaka kasuwantar da komai ciki harda Computer, anaso kagane ilmin kasuwa ta yadda kila kaine zaka zama Mark Zuckerberg ko Bill Gate na gobe.
4. Citizenship ko Civic Education: Anaso ka fahimci tsarin kasa saboda kila zaka iya zama dan kasuwa a harkar tech sannan zakaso fadada kasuwancinka zuwa wajajen amma dai kasan al’adu da dokoki wajaje sun banbanta.
5. Nigeria People and Culture: So ake fahimci ƴan Nigeria da Al’adunsu, misali tayu ka oya bude shafin saida giya a kudu, amma a Arewa fa? Kasan zaka zama abin zargi ko? Wannan shine manufar wato ka fahimci mutane daban dabanne ke rayuwa a Nigeria.
6. Phyiscs (Electronic): Mafi yawan darasin Physics da ƴan Computer ke dauka bangaren Electricity ne, Computer bata aiki sai da lantarki, kaga kuwa kana bukatar fahimtar yaya lantarki ke aiki a takaice da masalolin da ke iya jawowa Computer.
7. Numerical Analysis: Ana koyar dashi ne saboda kai dalibin Computer ka fahimci yadda zaka iya samarwa wadannan masalolin lissafin mafita ta hanya taqaitacciya. Numerical Analysis yana maida hankali ne kan Approximation na number. Shin kataba rubuta Looping a code yashiga Infinity Loop? Wato ya kasa tsayuwa? Manufar shine yadda zaka tsaida ita.
A yanzu wadannan sune darussan da sukazo kaina. Idan akwai wadanda na manta a rubuta su a comment.
Muhammad Baba Goni (Royalmaster)
13/05/2024.
Leave a Reply