YAU SHEKARU 57 KENAN DA KIRKIRO JIHAR KANO.
A Rana Mai Kamar Ta Yau 27 ga watan Mayu 1967 Gwamnatin Soja ta Janar Yakubu Gowon ta kirkiro jihohi guda 12 a Najeriya.
cikin har da jihar Kano.
Kwamishinan Yansanda Audu Bako Shi ne Gwamnan Jihar Na Farko.
Wannan jaha daga shekarar da aka ƙirƙire ta zuwa yau, ta samu jagorancin gwamnoni har goma 17 daga shekarar haihuwarta 1967 zuwa 2024.
Kafuwar Jahar Kano.
Shugaban mulkin soja, Manjo-Janaral Yakubu Gowon, shi ya ƙirƙiri jahar Kano tare da sauran wasu jahohi goma sha ɗaya a Ranar 27 Ga Watan mayu na shekarar 1967.
Babbar manufar Shugaba Yakubu Gowon ta kafa waɗannan jahohi ita ce kusanta jama’a da gwamnati da kuma kusanto da gwamnati ga jama’a. Wato kenan ya zama jama’a sun je kusa da gwamnati ita ma kuma gwamnatin ta kusancin jama’a.
Jahar Kano.
Bayan shekaru bakwai da samun ‘yancin kan Najeriya, wannan gari mai tarin albarka ya zama jaha, a cikin shekarar 1967.
Wannan jaha tana ɗaya daga cikin muhimman jahohin Najeriya, kuma kusan a yanzu ita ce cibiyar arewacin Najeriya ta fuskacin hada-hadar kasuwanci da siyasa. Ita ce jaha mafi yawan jama’a a duk faɗin Najeriya kamar yadda sakamakon ƙidayar jama’a da aka gudanar a 2005 ya tabbatar.
Leave a Reply