![]() |
Ƙaramin Bayani Akan Yadda Pre-market ɗin Exchanges Yake: |
Ƙaramin Bayani Akan Yadda Pre-market ɗin Exchanges Yake:
Indai a Exchanges kamar su Kucoin za’ayi Pre-market ɗin Hamster, kusan haka bashi da wani amfani ga wanda yayi Mining ɗin Hamster, tsarin ba irin Pre-market ɗin da akayi na Notcoin bane da mutane suka siyar suka amshi chanjin su na Voucher.
A Exchange in ka siya Coin a Pre-market, za’ayi maka freezing ɗin USDT ɗinka ne, baza’a sakar maka USDT ɗin ba, shima coin din bazai sauka wallet dinka ba har sai ranar da akayi launching ɗinsa a Exchange ɗin da kamar awa biyu ko uku.
Tsarin Pre-market da kowa zai amfana shine irin na Voucher ta Notcoin da akayi, wanda mutun zai iya zuwa ya siya ko ya siyar kuɗin sa su sauka nan take.
Leave a Reply