ƙirƙiro fasahar da matasa za su ga yadda za su zama idan sun girma

An ƙirƙiro fasahar da matasa za su ga yadda za su zama idan sun girma

Mutum-mutumi
ASALIN HOTON,LINKEDIN
Bayanan hoto,Mutum zai riƙa magana da mutum-mutumin da aka yi mai ƙwaƙwalwa kamar shi
Masana a jami’ar kimiyya da fasaha ta Massachusetts (Massachusetts Institute of Technology ) da ke Amurka, sun ƙirƙiro wata fasaha da za ta bayar da dama ga masu amfani da ita su iya yin magana da ƙirƙirarran mutum mai kamanninsu ta komai da ke zaman kamarsu idan sun girma.
Wanan fasaha da aka yi wa laƙabi da “Future You” an tsara ta ne domin ta taimaka wa matasa nazari a kan kansu da kuma burinsu domin bunƙasa tunani da hankalinsu.
Fasahar tana samar da lissafi ko tunani da zai kasance daidai da na mai amfani da ita, inda za ta zo da tunani kusan daidai da yadda shi wannan mutum zai yi idan ya kai shekara sittin a raye.
A nazarin farko da aka yi, masu amfani da fasahar sun nuna cewa sun samu raguwar fargaba, da kuma samun karin kauna da so da alaƙanta kansu da rayuwarsu ta gaba bayan ƴar tattaunawa da ƙirƙirarran mutum-mutumin.

Published on: June 6, 2024. at: 6:24 am

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*