Abin da ya kamata mutane su sani shi ne; ana bin Mazhaba ne a mas'alolin Ijtihadi, wato mas'alolin da babu Nassin Alkur'ani da Hadisi ko Ijma'i a kansu.

 Abin da ya kamata mutane su sani shi ne; ana bin Mazhaba ne a mas’alolin Ijtihadi, wato mas’alolin da babu Nassin Alkur’ani da Hadisi ko Ijma’i a kansu.

Abin da ya kamata mutane su sani shi ne; ana bin Mazhaba ne a mas'alolin Ijtihadi, wato mas'alolin da babu Nassin Alkur'ani da Hadisi ko Ijma'i a kansu.

Amma matukar aka samu Nassin Alkur’ani, ko Nassin Hadisi ingantacce, wanda Malaman Hadisi suka inganta shi, to babu maganar Bin wata Mazhaba a kan mas’alar, ko da Mazhabar Malik ne ko ta waninsa. Saboda maganar Allah da Manzonsa da Ijma’in Musulmai su ne hujja a Addini ba ra’ayin wata Mazhaba guda daya ba.

Kuma in ka soki Hadisin Azumin “Sittu Shawwal” da cewa; ai ba maganar Annabi ba ce, maganar Muslim ce, don haka sabani a kan Azumin “Sittu Shawwal” sabani ne tsakanin Muslim da Malik, to ai haka wani ma zai ce maka: duka Hadisan da suke cikin Muwadda’a Malik ba maganganun Annabi (saw) ba ne, maganganun Malik ne ko kuma na almajiransa. Da haka sai a rusa Hadisan Manzon Allah (saw) gaba daya.

Saboda haka a yi hattara, wannan makirar hanya ce ta rusa Addinin gaba daya, ko da kuwa ba rusa Addinin aka nufa ba.

Duk fa inda aka je aka dawo, inda tushen sabanin yake shi ne ka’idar nan ta Malikiyya, wacce suke soke Hadisai da ita, wato “Aikin Mutanen Madina”. Alhali wannar ka’ida ba hujja ba ce a wajen sauran Malamai. Ta yaya za ka soke Hadisi ingantacce a wajen Malaman Hadisi, Hadisin da Malamai suke ganin Mutawatiri ne da ka’idar da ba a yi Ittifaqi a kanta ba?!


Published on: June 8, 2024. at: 10:31 pm

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*