Albishirinku! Albishirinku! Albishirinku!
An Dora Rubutaccen Tafsirin Prof. Muhd Sani Umar R/lemo A Manhajar Play Store Da Apple Store.
Cibiyar Al-Basa’ir da kuma Cibiyar Al-Bayyinat manyan cibiyoyi ne na Duniya wadanda su ke hidima ga Al-kur’ani da dukkan abin da ya dangance shi. Sun dauki nauyin dora bakandamen Tafsirin nan mai suna: “Fayyataccen Bayani Na Ma’anoni Da Shiriyar Alkur’ani” Wallafar Babban Malaminmu Prof. Muhd Sani Umar Rijiyar lemo (Hafizahullah) a kan manhajar Play Store da kuma App Store. Wanda wannan na nuni da cewa mutum zai iya sauke wannan Tafsiri kai tsaye a wayarsa, ko a Computer domin amfana da shi a duk lokacin da ya so. Ba ya ga wasu abubuwa da Manhajar ta kunsa, sai kun shiga za ku gani.
Kamar yadda aka sani, wannan Tafsiri wagage an buga shi cikin Mujalladi (6) manya-manya, wanda shi ne mafi girman rubutaccen Tafsiri da aka tab’a samu a Tarihi cikin harshen Hausa. Allah Ya saka wa Malam da alkhairi.
Ga duk mai bukatar saukewa zai iya shiga wannna mahad’ar (Link)
https://hausaquran.net/ kuma abin sha’awa bai da nauyi, an yi masa aiki mai kyau, an kuma saukake saukar da shi, Megabyte nasa baki daya (13 MB) ne kacal! Ku hanzarta domin sauke shi a wayoyinku.
Mai Rubutu:
Malam Musa Muhammad Dankwano.
Sakataren Kwamitin Ilimi Na Prof. Muhd Sani Umar R/lemo.
11-06-2024.
Leave a Reply