Bayan ka karanta wannan bayanin baza ka sake installing pirated software akan computer ka ko wayar ka ba.

 

Bayan ka karanta wannan bayanin baza ka sake installing pirated software akan computer ka ko wayar ka ba.
Bayan ka karanta wannan bayanin baza ka sake installing pirated software akan computer ka ko wayar ka ba.  @KUMURYA MEDIA

Bayan ka karanta wannan bayanin baza ka sake installing pirated software akan computer ka ko wayar ka ba. 

According to Microsoft (2018), sun ce 67% na computer users a Nigeria suna amfani da pirated software. Idan akace software is pirated ana nufin jabu ko wanda aka sata akayi unlocking. Suka ce Microsoft word da Windows operating system su suka fi kowane software fuskantar kalubate. 

Illar amfani da pirated software sun hada:

1. Duk wani pirated software anyi altering program din sa. Don haka idan ka saka shi akan computer ko waya yana shiga yayi altering system registry da kuma programming settings. Hakan zai sa duk wani abu mai kyau da zaka saka wanda ba jabu ba, to zai wahala ya shiga.

2. Altering registry din computer da suke yi yana sa wasu malicious software din irin su malware duk kankantar su su samu wajen zama akan kwakwalwar na’urar. Ta yadda kowa zai iya hacking din ka ko ka sani ko baka sani ba.

3. Suna saka computer ko waya yin slow. Computer sai tayi minti 5 akan zaka bude word ko Adobe. Idan waya ce ta rika zafi kamar zata kone, sannan takan iya resetting kan ta da kan ta. 

4. A karshe solution shine ko dai kayi asarar operating system din ta hanyar sanya wani, ko kuma kayi System Reset. Don ko kayi system restore using a registered restore point, baya yi. Saboda registry has been altered. 

A duk sanda kake son installing Apps. Kowane App ko software da ka sani akwai free version din sa. Kayi downloading ya fiye maka sauki. Sannan a daina installing Software da aka samo daga torrent sites. Wannan ma sun fi hadari akan kowanne. 

Asuba ta gari.

Muhammad Ubale Kiru


Published on: June 11, 2024. at: 7:49 am

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*