![]() |
GOOGLE: WASU ABUBUWAN BAN MAMAKI DA ZAKA IYA GODAWA A GOOGLE YANZU @KUMURYAMEDIA |
GOOGLE: WASU ABUBUWAN BAN MAMAKI DA ZAKA IYA GODAWA A GOOGLE YANZU
1. Recursion
A Google idan kayi searching keyword “Recursion” Google zai nuna maka “Did you mean Recursion?” duk da dai dai aka rubuta a kalmar. Da ace za’ayi clicking link din did you mean din zai sake kawo maka Did you mean Recursion. Dalili shine Google zai nuna maka cikakkiyar ma’anar kalmar ne a practically, domin ma’anar recursion shine Loop wato maimaita abu, shiyasa da zara kayi searching din Recursion din “Did you mean Recursion?” Zai zama yana indefinite loop ta yadda zai sake maimaika shi ko da anyi clicking. Za’a iya godawa yanzu.
2. Askew
Kalmar askew a turanci na nufin abin baya dai dai gabarsa ko kuma abinda yake a karkace gefe daya. Idan har akayi searching keyword “Askew” za’aga Google Homepage ya karkata gefe daya maimakon asalin yadda yake.
3. Do a barrel roll.
Da zaran mutun yayi searching “Do a barrel roll” za’aga homepage din Google yayi rolling kamar tayar keke wato daga sama zaiyi zagaye zuwa kasa sannan yakoma yadda yake wannan duka yana nuna ma’anar abin.
4. Timer
A Google mutun na iya seta alarm dinsa da zaran lokacin yayi wayar mutun zai fara bugawa ko ince kara. Kamar daj yadda ake saita alarm haka shima, misali mutun yanaso yafita nan da 30 minutes sannan yana browsing yanzun haka yana iya saita timern Google saboda tunatar dashi.
4. Spinner
Zai baiwa mutun damar wasan spin kawai a rubuta “Spinner” ko “Google Spinner”
5. 100000000=english
Google yana iya fassarama mutun lambobi zuwa Turanci misali idan mutun ya rubuta 100000000=english
Google zai bashi answer One Hundred Billion.
6. Google Gravity
Da zaran mutun ya rubuta “Google Gravity”, Google zai kawo wani site Mai Suna Mrdoob idan akayi click aka shiga za’aga Homepage din Google anan duk abinda mutun ya taba za’aga Design din Google ya ruguzo kasa. Wannan yana nunawa mutun yadda Zero Gravity yake da kuma ma’anar ko yanayin Gravity.
Za’aga misali a hoton kasa.
7. Google Space
Shima kamar Google Gravityn yake kuma duka suna cikin Mrdoob shima zai nunawa yadda Design Google zai na nunawa idan mutun yaje space.
– Muhammad Baba Goni (Royalmaster)
05/06/2021
Leave a Reply