Wasu masu ƙwacen waya sun kashe Jami’in Soja a Kaduna
Rahotanni sun bayyana cewa wani sojan Najeriya Laftanar IM Abubakar ya rasa ransa sakamakon farmakin da wasu masu satar waya suka kai masa a Jihar Kaduna.
An tabbatar da cewa lamarin ya afku ne a yankin Unguwan Sarki da ke cikin Jihar Kaduna.
Zagazola Makama, wani kwararre ne kan yaki da ta’addanci a tafkin Chadi ya bayyana haka a cikin wani sakon da ya wallafa a shafinsa na dandalin X wato Twitter ranar Laraba.
Makama wanda ya bayyana lamarin a matsayin abin bakin ciki ya ce, Abubakar hazikin Jami’i ne.
Ya rubuta “Abin bakin ciki ne “Laftanar IM Abubakar (Isa) wani matashin Jami’in Soja ne mai hazaka, wasu barayin waya sun kashe shi a hanyarsa ta komawa gida a Unguwan Sarki Kaduna.”
“Allah ya jikansa da rahama”
Daga Lukman Aliyu Iyatawa
Leave a Reply