Ballon d’Or 2024: Rodrygo bai ji daɗi da baya cikin ƴan takara ba
Ɗan wasan Real Madrid, Rodrygo ya ce ya ji takaici da ba sunansa cikin ƴan takara 30 a ƙyautar Ballon d’Or 2024.
Mai sekara 23 ya ci ƙwallo 17 ya bayar da tara aka zuraa raga a wasa 51 a kakar da ta wuce a ƙungiyar Sifaniya.
Amma ɗan Brazil ba a bayyana shi cikin masu takarar bana ba, amma da sunan wasu takwarorinsa a Real Madrid da ya haɗa da Jude Bellingham da Vinicius Jr.
”Rai na ya ɓaci, ina jin ya kamata da sunana a cikinsu,” kamar yadda Rodrygo ya sanar da ESPN.
”Ban son na kaskantar da ƴan wasan da ke takara a bana, amma ina jin na cancanta cikin masu fatan lashe ƙyautar nan daga 30 da aka ware.
Ana fitar da ƴan takara ne daga editocin mujallar France Football tare da jakadan Ballon d’Or, Didier Drogba da wasu ƴan jarida.
Za a sanar da wanda zai lashe Ballon d’Or na 2024 karo na 68 a wani kasaitaccen biki da za a yi ranar 28 ga watan Oktoba a birnin Paris.
Rodrygo yana cikin ƴan wasan da suka bayar da ƙwazon da Real Madrid ta lashe La Liga da Champions League a bara.
Sauran da suke takara daga Real Madrid sun hada da Jude Bellingham da Vinicius Junior da Dani Carvajal da Federico Valverde da Antonio Rudiger da Toni Kross, wanda ya yi ritaya daga buga tamaula.
Ƙyaftin ɗin tawagar Faransa, Kylian Mbappe wanda ya koma Real Madrid daga Paris St Germain kan fara kakar bana, yana cikin ƴan takara 30.
Rodrygo ya ce rawar da yake takawa a Brazil da Real Madrid da ƙwazon da yake yi, ya dace ace yana cikin masu takarar Ballon d’or ta bana.
Leave a Reply