Kotun Kolin Ghana Ta Tabbatar Da Kudirin Yaki Da Luwadi Da Madigo

Kotun Kolin Ghana Ta Tabbatar Da Kudirin Yaki Da Luwadi Da Madigo
Image Source: Al Jazeera English News Website

 Kudirin ya yi tanadin daurin shekaru 3 ga wanda aka samu da laifin aikata luwadi ko madigo da kuma daurin shekaru 5 ga wanda aka samu da laifin daukar nauyin ayyukan ‘yan luwadi da madigo.

Kudirin ya yi tanadin daurin shekaru 3 ga wanda aka samu da laifin aikata luwadi ko madigo da kuma daurin shekaru 5 ga wanda aka samu da laifin daukar nauyin ayyukan ‘yan luwadi da madigo.

WASHINGTON DC — 

A yau Laraba, Kotun Kolin Ghana ta yi fatali da yunkurin da aka yi har sau na soke dokar da ake takaddama akanta wacce ta yi mummunan tanye hakkokin ‘yan luwadi da madigo da ‘yan majalisar kasar suka amince da ita a farkon shekarar da muke ban kwana da ita.

‘Yan majalisar sun amince da kudirin hakkin jima’i da tarbiyar iyali a watan Fabrairun da ya gabata, abin da ya janyo allawadai a fadin duniya duk da dimbin goyon bayan da ya samu daga kasar.

Kudirin ya yi tanadin daurin shekaru 3 ga wanda aka samu da laifin aikata luwadi ko madigo da kuma daurin shekaru 5 ga wanda aka samu da laifin daukar nauyin ayyukan ‘yan luwadi da madigo.

Kudirin zai iya zama doka ne kawai idan ya samu sa hannun Shugaba Nana Akufo-Addo, wanda har yanzu bai bayyana ra’ayinsa ba.

Tunda fari Akufu-Addo, wanda a hukumance zai sauka daga mulki a ranar 7 ga watan Janairu mai kamawa, yace zai jira yaga hukuncin da kotun kolin za ta yanke akan dacewar kudirin da dokokin kasar

Published on: December 18, 2024. at: 7:39 pm

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.

*