Abubuwa 15 Da Za Su Kankaro Maka Mutunci A Zamantakewarka Da Mutane:
1- Idan ka kira mutum a waya sau ɗaya ko biyu, amma bai ɗauka ba, kada ka sake kira, kuma ka kyautata masa zato, la’alla bai gani ba ne, ko kuma yana cikin yanayin da ba zai ɗauka waya ba, sai dai idan kana da tabbacin dalilin da ya sa bai ɗauka ba.
2- Ka mayar da kuɗi ko wani abu da ka ara, kada ka bari sai an tambaye ka.
3- Kada ka yi wa mutum tambaya da take da alaƙa da sirrin rayuwarsa, idan ma buƙatar hakan ta kama, to ka fara da neman izininsa.
4- Idan abokinka ya biya muku kuɗin mota ko abinci ko wani abu, to ka yi ƙoƙari ka biya muku na gaba.
5- Idan mutum yana magana kada ka katse shi, ka ba shi dama ya gama faɗin duka maganarsa koda ba ka yarda ba.
6- Idan ka yi wa mutum raha ko barkwanci, sai ka kula ba ya so, to kada ka sake, kuma ka nemi afuwarsa.
7- Idan mutum yana magana da kai, kada ka riƙa ba shi amsa alhali idonka na kan waya, zai ga ka raina shi.
8- Idan mutum ya gaya maka zai je asibiti, kada ka tambaye shi me zai je yi, ka yi masa addu’a kawai, idan yana son ka sani, zai gaya maka da kansa ba sai ka tambaye shi.
9- Kada ka riƙa saurin ba da shawara idan ba a nema daga gare ka ba.
10- Idan ka sanya glass mai duhu, to ka cire shi idan kana magana da wani.
11- Idan mutum ya ba ka wayarsa domin ka ga photo ko video ko wani abu, to kada ka yi scrolling gaba ko baya, don ba ka sani ba ko sirrinsa ne a wajen.
12- Idan ka fahimci ba a so ka ji magana, to koda ka ji, ka yi kamar ba ka ji ba.
13- Idan mutum ya yi kuskure a gabanka, sai ya yi sauri ya gyara, to ka yi kamar ba ka fahimci ya yi kuskuren ba.
14- Idan mutum ya ɗauki nauyin biya maka kuɗin abinci ko wani abu, kada ka ɗauki mai tsada sosai.
15- Idan mutum ya rubuta abin da ya burge ko ya amfanar da kai, amma ba ka yaba masa ba, to idan ya rubuta wanda bai burge ka ba, kada ka soke shi, hakan ƙaranta ne.
15/01/2025
✍️ Isa Sadi
Leave a Reply