AAMIR KHAN YA BAYYANA CEWA BAYA KARBAR KUDIN AIKI TSAWON SHEKARU 20 :
‘Ina Samun Riba Ne Idan Fim Ya Yi Nasara’
Aamir Khan, wanda ya sake fasalin al’adar masana’antar fina-finai a cikin shekaru 37 da suka gabata, ya yi bayani game da aikinsa, gazawarsa, da kuma salon samun kudinsa a taron ABP News. Yayin da yake shirye-shiryen cika shekaru 60 a watan gobe, fitaccen ɗan wasan kwaikwayon ya yi bayani kan tafiyarsa da kuma tsarin kudin da yake amfani da shi a fina-finansa.
Lokacin da aka tambaye shi game da dalilin da yasa yake ci gaba da gwaji da nau’ikan rawar da yake takawa, Aamir ya bayyana wata babbar gaskiya game da albashinsa. Ya ce:
“Tun cikin shekaru 20-21 da suka gabata, ba na karɓar kuɗin aiki daga fim. Idan fim ɗin ya yi nasara, sai na samu riba, idan kuwa bai yi ba, to ni ma ba na samun komai.”
Ya bayyana cewa yana amfani da tsohuwar hanyar samun kuɗi da ’yan wasan kwaikwayo a Turai ke amfani da ita tun da daɗewa. Wannan ya bashi damar samun ’yanci da yin gwaji da fina-finai masu ƙalubale.
Wannan dabara tasa ta ba Aamir Khan ikon fitar da fina-finai masu ma’ana, yana fifita inganci fiye da samun riba kai tsaye.
#AshiruAamirian #AshiruBujawa #AamirKhan #Mrperfectionist #AamirKhanFansNigeria
Leave a Reply