AN ƘARA BUƊE SHAFIN NEMAN BASHIN KARATU (NELFUND) NA KAKAR KARATUN 2024/2025

AN ƘARA BUƊE SHAFIN NEMAN BASHIN KARATU (NELFUND) NA KAKAR KARATUN 2024/2025
Asusun bada lamunin karatu ga Ɗaliban Manyan Makarantun Najeriya (NELFUND) ya sanar da ƙara buɗe shafin neman bashin karatu ga dalibai a kakar karatu ta 2024/2025, bayan garƙame shafin neman bashin a kakar karatu ta 2023/2025 da asusun yayi da yammacin jiya.
• MENENE NELFUND – KUMA MENENE ALFANUNSA GA ƊALIBAI ?
NELFUND tsari ne na bada lamuni ga Ɗaliban da ke karatu a Manyan Makarantun Ƙasar nan, Wanda ya haɗarda kuɗin kula da kai a makaranta (upkeep) – Naira 20,000 a kowanne wata ga Ɗaliban da su ka samu nasarar shiga cikin shirin.
 Da kuma biya musu kuɗin makaranta 100 bisa 100, a matsayin lamuni marar ruwa, wanda za a fara biya bayan shekaru biyu da kammala hidimar ƙasa (NYSC).
WA YA CANCANTA YA NEMI BASHIN ?
• Dukkannin Ɗalibin da ke karatu a kowacce ɗaya daga cikin manyan makarantun ƙasar nan (Polytechnics, Colleges Of Education, Colleges Of Health, Universities etc)
KU SANI: Kowanne Ɗalibi Zai Iya Nema – Ko Da Yana Karatu A Makarantar Gwamnatin Tarayya Ne Ko Ta Jiha.
Haka zalika, waɗanda basu ci gajiyar shirin a zangon karatun 2023/2024 da ya gabata ba ma, suna da dama neman wannan.
ME DA ME AKE BUƘATA A LOKACIN NEMAN BASHIN ?
• JAMB Registration Number
• NIN 
• BVN
• Sunan Makaranta Da Registration Number 
• Hoto
• Shekarun Ɗalibi, Jinsinsa, Lambar Wayarsa, Adireshin Gidansu, da Adireshin Email
• School ID Card
• JAMB Admission Letter.
TOH! ME KUKE JIRA ? – MUDDIN KUN MALLAKI DUKKANNIN WAƊANNAN ABUBUWAN DA MUKA LISSAFA:
Kawai ku tuntuɓi sashen Educational Consultancy Na Kamfanin Pandancy Global Technologies Ltd ta waɗannan hanyoyin, domin cike muku, Akan Sassauƙan Farashi:
• WhatsApp: 08121124840
Email: pandancyglobaltech@gmail.com
Kira: 08039411956
KU HANZARTA – DOMIN DA ZAFI-ZAFI AKE DUKAN ƘARFE!

Published on: February 24, 2025. at: 9:34 pm

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*