Atletico Madrid na zawarcin Nunez, Ƙungiyoyin Saudiyya na son Vinicius

 

Atletico Madrid na zawarcin Nunez, Ƙungiyoyin Saudiyya na son Vinicius

Atletico Madrid ta shiga zawarcin ɗan wasan Liverpool da Uruguay, Darwin Nunez mai shekara 25. (Caught Offside)
Liverpool na iya sayar da Nunez a lokacin baraza indai ta samu mai maye gurbinsa, inda ake tunanin ɗan wasan Brighton da Brazil, Joao Pedro mai shekara 23. (Teamtalk)
Ɗan wasan gaba a Brazil, Vinicius Jr na da damar samun fam miliyan 200 idan ya amince ya je Saudiyya a lokacin bazara duk da cewa matashin mai shekara 24 da sauran shekara biyu a kwantiraginsa da Real Madrid. (Telegraph – subscription required)
Tottenham za ta gwada sa’arta kan ɗan wasan Crystal Palace, Eberechi Eze mai shekara 26 da ke bugawa Ingila wasa. (Give Me Sport)
Manchester City na duba yiwuwar daidaitawa da ɗanw asan Faransa, Theo Hernandez mai shekara 27 wanda har yanzu bai kama daidaita sabon kwantiraginsa ba da AC Milan. (Teamtalk)
AC Milan ta soma bibbiyar ɗan wasan Wolves da Algeria, Rayan Ait-Nouri mai shekara 23, domin ya maye gurbin Hernandez. (Gazzetta dello Sport – in Italian, subscription required)
Ɗan wasan Porto, Samu Aghehowa ya kasance wanda Aston Villa ke hari, duk da dai matashin mai shekara 20 daga Sifaniya ya kasance wanda ƙungiyoyi irinsu Chelsea da Arsenal da West Ham ke farauta. (Caught Offside)
Sabon kocin West Ham Graham Potter na kokarin ganin yadda zai shawo kalubalen da yake fuskanta da Barcelona a cinikin ɗan wasan Canada Jonathan David mai shekara 25, da ke taka leda a Lille. (Give Me Sport)
Dole Manchester United ta biya fam miliyan 20 ga kocinta da ma’aikatansa muddin ta shirya korarsu. (Mirror)
Ɗan wasan gefe a Amurka Christian Pulisic, mai shekara 26, na gab da cimma yarjejeniyar sabon kwantiragi da AC Milan. (Gazzetta dello Sport – in Italian)
Chelsea na shirin tattaunawa da wakilan ɗan wasan River Plate, Ian Subiabre mai shekara 18 daga Argentine. (Give Me Sport)
Lyon ta kai karar PSG gaban hukumomin Lig din Faransa kan cikin ɗan wasan Georgia, Khvicha Kvaratskhelia, mai shekara 24. (L’Equipe – in French)

Published on: February 27, 2025. at: 5:42 am

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*