Ilimin Taurari Ko “Zodiac sign” A Yau da jiya..

Ilimin Taurari Ko “Zodiac sign” A Yau da jiya..
Duk Ilimin taurarin nan da mutanen da Larabawa da Turawa da Hausawa da sauran ƙabilu suka ɗauka suke ƙafafa da shi rankatakaf ɗinsa daga Mutanen Girka ya fita sai amma a yau sai ka samu wani baƙin tukururu ya laɓe a soro ya zuba ƙasa a kwali yana karɓe kuɗin mutanen da niyyar yana bugawa mutane ƙasa yana basu Sa’a akan al’amuran rayuwarsu ko yana duba musu taurarin su.
Wannan duk Ilimine na girkawa tun kafin Haihuwar Annabi Isa sai bayan dubun nan shekaru sannan Larabawa suka sato suka fassara zuwa Yaren su, suma hausawa suka rarumo wajen Larabawa suke Shan jar miya da harkar.
Malamin da ya fara Kwaso wannan Fasaha daga girkawa shine.
1-Abu Ma’shar Al-Balkhi (787–886 AD)
Ya kwaikwayi ayyukan Ptolemy da Dorotheus na Sidon, ya fassara su kuma ya haɓaka su.
Ya rubuta Littafin Larabci mai suna “Kitab al-Mudkhal ila Ilm Ahkam al-Nujum”.
Amma fa ka gane akwai banbanci tsakanin Ilimin “Zodiac Sign
2. Al-Kindi (801–873 AD
3.Al-Biruni (973–1048 AD)
Ya rubuta “Kitab al-Tafhim li Awa’il Sina’at al-Tanjim”, wanda ya ƙunshi bayanai kan astrology da astronomy.
Sai oga Gagarabadau “.
 Al-Farabi (872–950 AD)
Duk wani Masanin Taurari ɓangaren “Astrology Indai Kai Musulmi ne waɗannan mutanen dana lissafa sune Magabatanka sune suka fara kawo wannan ilimi cikin duniyar Musulunci kuma dukkansu daga Masana manyan Malaman girkawa suka Kwafo su ma basu yi shakkar hakan ba.
Waɗannan malaman Larabawa sun kwaikwayi astrology daga masanan Girka kamar Ptolemy da Aristotle.
Amma ina ji da yawa daga bakin mutanen mu Hausawa suna nuna cewa larabawa sune ma suka kawo ilimin Taurari na “astrology” Wanda hakan zallar nuna rashin sani ne. Larabawa dai suna son ƙwace Harkar ne kawai amma asali basu san komai akai ba.
Shi Kansa “Astrology da Larabawa suke ƙafafa akansa kaso 50 Na sa babu hujja a cikin Ilimin, Kuma ya Kamata Ka banbance tsakanin Astrology da Astronomy suna da bambanci kada kace nace kaso 50 ba gaskiya bane ina maganane kawai akan astrology ban da Astronomy.
Meye Banbanci Astrology da Astronomy?
1. Astronomy (Ilmin Sararin Samaniya)
Ilimi ne na kimiyya da ke nazarin taurari, duniyoyi, da sauran abubuwan sararin samaniya.
Yana amfani da lissafi, kimiyya, da fasaha don fahimtar yadda sararin samaniya ke aiki.
Masana kamar Galileo da Einstein sun ba da gudunmawa a wannan fanni.
Wannan babu Inkari akansa.
Shi Kuma Astrology Wanda muke magana akai shine.
Ilimi ne da yake cewa “Wai” motsin taurari da duniyoyi suna da tasiri a rayuwar mutane. Ma’ana Rayuwar mu anan duniya tana Connecting da rayuwar Taurari da sauran duniyoyi Kamar su Venus, Saturn, Jupiter da sauransu dai.
Bashi da tushe na kimiyya, kuma yana dogara ne akan tsoffin imani da tsarin zodiac (Kamar Aries, Taurus, Gemini, da sauransu).
Ana amfani da shi don fassara halayyar mutum da Hasashen Rayuwar Mutum abubuwan da za su faru a rayuwarsa da Kuma Halayensa.
Kamar Yadda Girkawa suka kasa taurarin Gida 12 kuma kowanne mutum yana da alaƙa da su kwatancin Watan da aka haifeshi da shekarar haihuwarsa sune Kamar haka .
♈ Aries – Κριός (Krios) – الحمل (Al-Ḥamal)
♉ Taurus – Ταύρος (Tavros) – الثور (Ath-Thawr)
♊ Gemini – Δίδυμοι (Didymoi) – الجوزاء (Al-Jawzāʾ)
♋ Cancer – Καρκίνος (Karkinos) – السرطان (As-Saraṭān)
♌ Leo – Λέων (Leon) – الأسد (Al-Asad)
♍ Virgo – Παρθένος (Parthenos) – العذراء (Al-ʿAdhrāʾ)
♎ Libra – Ζυγός (Zygós) – الميزان (Al-Mīzān)
♏ Scorpio – Σκορπιός (Skorpios) – العقرب (Al-ʿAqrab)
♐ Sagittarius – Τοξότης (Toxótis) – القوس (Al-Qaws)
♑ Capricorn – Αιγόκερως (Aigókeros) – الجدي (Al-Jady)
♒ Aquarius – Υδροχόος (Ydrochóos) – الدلو (Ad-Dalw)
♓ Pisces – Ιχθύες (Ichthýes) – الحوت (Al-Ḥūt).
Kowanne ɗan adam kamar yadda ilimin yace yana ɗaya daga cikin wannan taurarin ya danganta da watan da aka haifeka daga January Zuwa December ‘.
Irin wannan masu ilimi su ake kira da ƴan bugun ƙasa ko duba ko ilimin taurari.
Irin su ne Masu Karɓe kuɗin mutane don duba musu sa’arsu ko faɗa musu abubuwan da zai iya faruwa a rayuwarsu nan gaba suna dubawa ne bisa’ la’akari da yadda taurari suke da kuma yadda duniyoyi ke juyawa a loƙacin.
Wannan ilimi sam bashi da alaƙa da kowanne addini kuma ba ilimi bane wanda za’ace an yadda dashi ɗari bisa ɗari.
Kuma kada wani Mai tara ƙasa jibge a gabansa ya raina maka wayo ya dinga karɓe maka kuɗaɗe a banza shima bashi da tabbas don babu wanda ya tabbatar da sahihancin wannan ilimi.
Al-Biruni (973–1048 AD), Babban Masani a wannan ilimi na Astrology yace fa babu hujja ƙwaƙwƙwara dake tabbatar da wannan ilimi Rauninsa yafi tabbas ɗinsa.
Haka Manyan Masana kamar su
Al-Farabi (872–950 AD)
Shine Duniya ta tabbatar yafi Kowa sanin Wannan ilimi amma shima ya tabbatar wannan ilimi babu tabbas cikinsa.
Averroes (Ibn Rushd) (1126–1198 AD)
Ya ce ilimin astrology bashi da wata alaƙa da kimiyya ko kusa da gaskiya kawai yana jirkita tunanin mutane ne daga asalin gaskiya.
Don Haka idan zaka je wajen ɗan duba kaje kana sani..
Ni a wajena da Maganar ɗan duba da Waƙar Ali Makaho ba banbanci.
Allah Ghalib.

Published on: February 26, 2025. at: 7:08 pm

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*