Sanarwa Daga CUPS!
Jama’a barkanmu da warhaka. Ina murnan sanardaku cewa registration form na karatun Computer and ICT na CUPS ya fito. Kowa da kowa zai iya cikewa. Mazauna kudu da kasashen waje suma suna iya cikewa. Kuna iya cike form din da salula ko da computer.
Registration kyauta ne. Horaswa na sati goma sha biyar (15) shima kyauta ne. Laboratory hands-on experience shima kyauta ne. Daga karshe, duk wadda yayi kokarin kammala training har na tsawon sati 15, zai sami Certificate daga kassaitaccen Jami’a. Wannan Certificate din shima kyauta ne.
Muna da kudurin training matasanmu da zawaranmu da marayummu su dubu dari (100,000) a zagaye na farko. Toh amma daga bisani muna fatan zamuyi training mutane million daya (1,000,000).
Jama’a ku duba a sashen comments akwai link na registration form din. Zamu saka link din kuma a dandalinmu na Telegram.
Jama’a don Allah kada kuyi watsi da wannan daman. Kudin horaswa da laboratory hands-on experience da certificate ya kai kamar naira dubu dari (N100,000).
Jama’a na barku lafiya.
Dr. Idris Ahmed.
CUPS.
16/2/2025.
I register a nan
Leave a Reply