Rukuni hudu na masu kallon fim din Hausa.

Rukuni hudu na masu kallon fim din Hausa.
1. Jemagu: Wannan rukunin mafi yawa ‘yan boko ne, da kuma masu karyar boko wadanda ba wai fim din Hausa ba, su duk wani abu da ya shafi Bahaushe ba sa kaunarsa. Irin wadannan rukuni sun fi kaunar finafinan turawa, kai sun fi fifita fim din mutanen Kudancin Najeriya fiye da na Hausa. Su fim duk ma’anarsa da kyawunsa in dai na Hausa ne za su caccake shi ko da kuwa ba su tsaya sun ga abin da ke cikin sa ba.
2. Tattabaru: Wadannan rukunin ‘yan gargajiya ne, ‘yan alkawari, su duk wani abu da ya shafi Hausa suna kaunarsa. Don haka duk irin fim din da aka yi da Hausa duk rashin kyawunsa da rashin ma’anarsa su suna jin dadin kayansu. Da yawa daga cikin su, suna da karancin ilimin zamani da kuma wayewa ta zamani. Don haka ko da fim ya zo da shirme ko shashashanci, kai ka jiyo, domin kai kake gane shirmen da shashancin, su kallon abin su za su yi, kuma babu abin da ya shafe su, domin abin da ke cikin fim din yayi daidai da saitin kwakwalwarsu. Irin su ne za ka yi fim, kana ganin yayi ma’ana sosai a mahangarka, amma su sai su ce bai musu kyau ba. Kai kuma in ba ka fahimce su ba sai ka yi ta fada kana cewa ga fim mai ma’ana sun ki kallo, to ai bai yi daidai da kwakwalwarsu ba ne Malam.
5. Dakilai: Wannan rukunin suna kamanceceniya da rukunin dakilan mutane (marasa sha’awa). Domin su ba su ma san menene dadin fim ba. Da wanda yayi kyau da wanda bai yi kyau ba, da wanda yayi ma’ana, da wanda aka tafka shiririta su duk daya ne a wajen su. Ana iya samun rukunin wadannan ‘yan kallo a cikin jahilai da masu ilimi, ‘yan kauye da ‘yan birni, wayayyu da kidahumai, ko ina akwai irin wadannan mutane. Haka nan irin wannan mutane za ka ga idan ana kallon fim ana ta ihu ana jin dadinsa ko kuma ana ta tsaki fim ya bata wa mutane rai, za ka ga su babu wani sauyi a fuskarsu, domin a wajensu duk daya wai makaho ya yi dare.
4. Gwanaye: Wannan kwararrun ‘yan kallo ne, wadanda ke dauke da rariyar tata a cikin kwanyarsu. Irin wadannan rukunin ‘yan kallo na iya kallon fim din Hausa, ko na yammacin duniya, ko na gabashin duniya kai ko wanne irin fim ma suna iya kallo, amma suna da zabi, ba komai suke kallo ba. Su, in dai fim yayi ma’ana yayi kyau to ko daga ina yake za su kalle shi kuma za su yaba masa. Mafi yawan su sun fi daga cikin masu ilimin zamani, amma a kan sami tsirari daga masu karancin ilimin zamani, amma wadanda ke da budewar idanu ta yawon duniya. 
Wannan tunanina ne, idan kana da naka, to mu hadu a comment section na san kai ma ko ke ma ba za ki rasa wani karin rukunin ‘yan kallon na fim din Hausa ba.

Published on: February 9, 2025. at: 7:10 am

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*