Shin Da Gaske Jaruman India Basa Kallon Fina-finan Da Yan Uwansu Suke Yi
Mutane suna yawaita tambaya wai jarumai suma suna kallon fina finan su bayan an gama dauka, eh tabbas za’a ce suna kalla fiye ma da yadda sauran mutane suke kalla saboda hakan ma nadaya daga cikin abunda ke kara musu kwarin gwiwa sosai, musamman ma ace shirin ya karbu sosai agun mutane, wasu kuma sai suke ganin a’a basa kalla saboda ai sun san duk abun da akayi aciki, to zancen gaskiya ba haka abun yake ba dalilin kuwa shine alokacin da ake daukar yawancin su fa hankalin baya jikin su musamman ma ace akwai irin role’s din nan masu wahala.
Lokacin da ake dauka bayan duk wata fita shi director yana bada damar a tsaya domin jarumi ko jaruma suga kuskurensu sannan suga yadda sukayi kokari, in kuma ma daukar batayi kyau ba to ana sake tana gaba daya. Amma ana samu daga irin natural actors din nan sau daya ake yi musu dauka shikenan an wuce wajen, wannan ina magana ne akan wajen daukar sabon shiri kuma akan kokwanton da wasu suke yi akan cewa yawancin jarumai basu cika kallon fina finan su ba.
To tabbas opposite side na wannan mahawarar shine yawancin su suna kalla domin suna kara samun kwarin gwiwa da kara kokari akan hakan.
Sai kuma batu akan yadda jarumi yake ji idan sabon shirin sa ya fadi da kuma yadda suke ji idan sabon shirin su yayi nasara. To wannan maganar kusan abune da kowa zai iya yanke hukunci akan ta don abune da yake a fili amma fa ta wata fuskar ba kowa ne zai iya yanke hukuncin ba , to amma zan dan taba sharhi kadan adangane da wannan lamari:-
Mufara daga kan yadda suke ji yayin da akace shirin su ya fadi, gaskiya abune wani yanayine wanda zan iya cewa kusan baya yi musu dadi wasu lokutan hakan yana sa suji cewa dole in an sake neman su awani shirin su maida hankali suyi abunda yakamata, wasu sukan ji cewar sufa basu da Kwarewa akan irin wannan bangaren kamar yadda nafada a rubutuna na jiya, to gaskiyar zancen dai itace jarumi yana jin ba dadi ayayyin da shirin sa ya fadi.
Sai kuma mu koma kan yadda suke ji idan sabon shirin su yayi nasara, yanayine wanda kaima ka san dole yayi musu dadi, shi yasa abaya nace hukunci ne wanda kowa ma zai iya yanke shi, tunda abune a fili kuma ma sunfi dagewa sosai wajen ganin koda an nemesu a shiri na gaba zasu yi abunda yafi wannan musamman ma ace sune zabin farko, Wannan shine.
Leave a Reply