Marigayi Shugaban Kasar Libya Muammar Gadafi Yana Duba Barnar Da Harin Amurka Ya Haifar A Gidansa Dake Birnin Benghazi Na Kasar
Tun a shekarun 1960, alakar Amurka da Libya ta tabarbare sakamakon zargin libya da ayyukan ta’addanci da zargin safarar makamai da kuma leken asiri. Takaddama tsakanin kasashen biyu ta yi tsami ne a shekara ta 1986.
A watan Janairun shekarar 1986 Amurka ta yanke huldar jakadanci da kasar Libya. A cikin watan Maris, sojojin ruwan Amurka sun mayar da martani bayan da sojojin Libya suka harba makami mai linzami kan jirgin ruwan kasar.
A ranar 2 ga Afrilu, 1986, gwamnatin Amurka ta zargi Libya da alhakin mutuwar mutane hudu a lokacin da wani bam ya tashi a jirgin TWA mai lamba 840 a kan birnin Argos na kasar Girka. A karshe ‘yan ta’adda sun kai harin bam a dandalin La Belle Discotheque da ke yammacin Berlin a ranar 5 ga watan Afrilu, inda suka kashe sojan Amurka daya tare da raunata fiye da mutane 200. Amurka ta yi iƙirarin “haƙiƙa, akwai ƙarfaffiyar shaida cewa kasar Libya ce ta kitsa harin, kuma ba tare da bata lokaci ba ta aiwatar da hari a kan birane biyu na Tripoli da Benghazi a kasar ta Libya, aikin da ta sanyawa suna Operation EL DORADO CAYON.
Operation EL DORADO CANYON ya kasance hari a “cibiyoyin da Amurka ta kira da na ‘yan ta’adda” a Libya. Harin anyi shi da jiragen yaki guda 48. An fara kai harin ne a ranar 14 ga Afrilu, 1986, lokacin da jiragen yakin sojojin saman Amurka suka tashi daga Royal Air Force (RAF) Base Lakenheath.
Da misalin karfe 7:00 na dare jiragen sojojin saman sun kai hari filin jirgin sama na Benina da kuma barikin sojan Benghazi, yayin da jirgin sama kirar F-111 guda 13 suka kai hari a barikin Aziziyah da ke Tripoli da kuma sansanin horar da dakarun gwagwarmaya a Sidi Bilal. Jiragen yakin sama na F-111 guda biyar ne suka kai harin na karshe a tawagar, wadanda suka kai hari a filin saukar jiragen sama na soji a Tripoli.
Bayan harin da aka kai, an samu rahotannin cewa an harbo jirgin F-111 guda daya. Daga baya an tabbatar da kashe matukan jirgin biyu.
Harin ya yi sanadiyar mutuwar mutane 37 (ciki har da wata jikar Gadafi yar shakara 9) tare da jikkata mutane 93. Shugaban Libya Muammar Kaddafi ya bayyana bacin ransa a fili, lokacin da ya bayyana a gidan talabijin, bayan sa’o’i 24 da kai harin don yin alawadai da hare-haren.
Leave a Reply