Tsokaci: Bayani game da banbancin maniyyin ɗa namiji da ƙwan mace.

Bayani game da banbancin maniyyin ɗa namiji da ƙwan mace.
Maza suna iya haihuwa tun bayan balaga har ƙarshen rayuwarsu, suna samar da ‘rayayyun, miliyoyin maniyyi kullum.
A gefe guda, haihuwar mata tana da iyaka, Mata suna fara haihuwa daga balaga zuwa lokacin sayawan al’ada (menapause)
Ana haifar da mata da kimanin ƙwayayen haihuwa miliyan ɗaya, amma ƙwayayen basa karuwa, kowanne wata mata na sakin ƙwai kwaya ɗaya kawai wanda ke da damar rayuwa da bai wuce na awa 12 zuwa 24 ba, yayin da maniyyi zai iya rayuwa a cikin mahaifa na kwanaki 2 zuwa 3.
Haihuwar mata tana raguwa daga shekara 30, inda damar samun ciki ke sauka daga kaso 25% kafin shekara 30 zuwa kaso 5% bayan shekara 40.
Haihuwar maza ma tana raguwa daga shekara 40 zuwa 45 saboda raguwa na sinadarin testosterone da ingancin maniyyi.

Published on: February 26, 2025. at: 7:14 pm

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*