Yan Ta’addan Boko Haram Sun Kai Hari a Borno, Sun Yi Gagarumar Barna

Yan Ta’addan Boko Haram Sun Kai Hari a Borno, Sun Yi Gagarumar Barna 
 Ƴan ta’addan Boko Haram sun kai farmakin ta’addanci a wani ƙauyen jihar Borno da ya yi shekara da shekaru ana fama Tsagerun ƴan ta’addan na Boko Haram sun kai harin ne a ƙauyen Kaleri na ƙaramar hukumar Mafa, suka yi awon gaba da mutum biyu Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Borno, ya tabbatar da aukuwar lamarin inda ya ce ana ci gaba da gudanar da bincike 
Jihar Borno – Wasu da ake zargin ƴan ta’addan Boko Haram ne sun kai hari a ƙauyen Kaleri da ke ƙaramar hukumar Mafa a jihar Borno. Ƴan ta’addan a yayin harin sun sace mutane biyu tare da kwashe dukiyoyi daga gidajen mazauna yankin. 
Jaridar The Punch ta rahoto cewa maharan ɗauke da makamai sun mamaye ƙauyen ne da yammacin ranar Talata. 
Ƴan ta’addan sun buɗe wuta ba ƙaƙƙautawa, lamarin da ya tilastawa jama’a guduwa don tsira da rayukansu. Ƴan sanda sun yi magana kan harin Boko Haram Mai magana da yawun ƴan sandan jihar Borno, ASP Nahum Daso, ya tabbatar da harin, inda ya bayyana shi a matsayin yunƙurin yin garkuwa da mutane. “An kai hari a Kaleri. Wasu da ake zargin ƴan Boko Haram ne suka kutsa cikin wani gida suka yi garkuwa da mutane biyu.” – ASP Nahum Daso Da aka tambaye shi ko an tura ƙarin jami’an tsaro zuwa yankin, sai ya ka da baki ya ce: 
Ana ci gaba da bincike, kuma zan tuntuɓi DPO don samun ƙarin bayani domin sanar da jama’a.” Majiyoyi sun yi bayani kan harin Wani mazaunin garin da ya buƙaci a sakaya sunansa saboda dalilan tsaro ya bayyana cewa maharan sun shigo da manyan makamai kuma sun yi ta kwasar kayan abinci daga gidaje daban-daban. 
“Da isowarsu, sai suka fara harbe-harbe, hakan ya sa kowa ya tsere. Bayan komai ya lafa, sai muka gano cewa sun tafi da mutane biyu.” – Wata majiya Wata majiya kuma ta tabbatar da cewa maharan sun bi gida-gida suna bincike, inda suka riƙa kwasar abinci da dukiyoyin mutane kafin su tsere. “Sun shigo da yawa, sannan sun ɗauki kayayyaki da dama kafin su bar ƙauyen.” – Wata majiya Bayan harin, jami’an tsaro sun kewaye yankin kuma sun cafke wasu mutane da ake zargi. Sai dai har yanzu ba a tabbatar da ko mutanen da aka kama na da alaƙa da harin ba. 
Ba a samu tabbacin sunayen mutanen da aka sace ba har zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoton. 

Published on: February 28, 2025. at: 6:24 am

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*