Za a ware ma MATA kujeru na DINDINDIN a zauren Majalisar tarayya da na jihohi waɗanda Mata ne kawai za su yi takarar kujerun.
____________________________________________
A shekarar 2022, cikin ƙasashe 187 da muke da su a duniya waɗanda su ke da zauren majalisa a tsarin gwamnatin su to Najeriya ita ce ƙasa ta 183 da suke da qarancin wakilcin Mata a zauren majalisa, a yankin Africa kuma Najeriya ce ƙasa ta ɗaya wajen rashin samun Mata a zauren majalisar, ita Kuma ƙasar Rwanda ita ce tafi kowace ƙasar da ke Africa yawan Mata a zauren majalisa kasancewar kashi sittin da ɗaya da ɗigo Ashirin da biyar (61.25%) na mambobin Majalisar duka Mata ne, ita kuma Najeriya kashi huɗu da ɗigo biyu ne kacal Mata a zauren majalisar (4.2%) wanda hakan ba ya rasa alaƙa da addini da al’adar mutanen ƙasar musamman yankin Arewa kasancewar su ne suka fi kowanne yanki yawa a ƙasar.
Tun bayan da aka shiga jamhuriyya ta huɗu a shekarar 1999 har zuwa yau (2025) kimanin shekara 25 kenan ana mulkin dimukraɗiyya, a cikin waɗannan shekarun ‘yan Najeriya sun zaɓi ‘yan majalisar Dattijai kimanin ɗari bakwai da sittin da uku jimilla, amma a cikin su Mata arba’in da uku ne kacal aka taɓa zaɓa a matsayin ‘yan majalisar Dattijan wato kashi biyar da ɗigo sittin da huɗu kenan (5.64%) a cikin shekara 25 da suka gabata. A majalisar wakilai kuma a cikin waɗannan shekarun (25) an zaɓi ‘yan majalisar wakilai jimilla guda dubu biyu da ɗari biyar da Ashirin (2,520 lawmakers) amma a cikinsu Mata ɗari da talatin da biyu ne kacal (132 women) aka zaɓa a cikin waɗannan Shekarun, wato kashi biyar da ɗigo Ashirin da huɗu kenan (5.24%) wanda hakan yake nuna ƙarancin da ake samu wajen shigar Mata harkokin siyasa a ƙasar. Don haka, a zaɓen da ya gudana a shekarar 2023 Mata huɗu ne kacal suka samu damar shiga zauren majalisar Dattijai a matsayin wakilan al’umma daga cikin ‘yan majalisar da adadin su yakai 109, wato kashi uku da ɗigo sittin da bakwai kenan (3.67%) Matan su ne:
1• Senator Ireti Heebah Kingibe
Daga FCT Abuja a ƙarƙashin Jam’iyyar Labour Party (LP)
2• Senator Adebule Idiat Oluranti
Daga Jihar Legas a ƙarƙashin Jam’iyyar APC
3• Senator Banigo Ipalibo Harry
Daga Jihar Rivers a ƙarƙashin Jam’iyyar PDP
4• Senator Natasha Hadiza Akpoti
Daga Jihar Kogi a ƙarƙashin Jam’iyyar PDP
A majalisar Wakilai kuma an samu Mata guda goma sha bakwai da suka samu damar shiga zauren majalisar wakilai domin wakiltar al’ummarsu a cikin ‘yan majalisar wakilan da yawan su ya kai 360 wato kashi huɗu da ɗkgo saba’in da biyu kenan (4.72%) duk da dai Hon. Onanuga ta rasu a ‘yan kwanakin nan Wanda Hakan ya sa suka Koma su Goma sha shida, Matan su ne:
1• Hon. Beni Butmak Lar.
Daga jihar Plateau a ƙarƙashin Jam’iyyar PDP
2• Hon. Boma Goodhead
Daga jihar Rivers a ƙarƙashin Jam’iyyar PDP
3• Hon. Khadija Bukar Abba Ibrahim
Daga jihar Yobe a ƙarƙashin Jam’iyyar APC
4• Hon. Zainab Gimba
Daga jihar Borno a ƙarƙashin Jam’iyyar APC
5• Hon. Blessing Onyeche Onuh
Daga jihar Benue a ƙarƙashin jam’iyar APC
6• Hon. Adewunmi Oriyomi Onanuga
Daga jihar Ogun a ƙarƙashin Jam’iyyar APC (Ita ce Allah ya yima rasuwa)
7• Hon. Miriam Odinaka Onuoha
Daga jihar Imo a ƙarƙashin Jam’iyyar APC
8• Hon. Tolulope Akande Sadipe
Daga jihar Oyo a ƙarƙashin Jam’iyyar APC
9• Hon. Kafilat Ogbara
Daga jihar Legas a ƙarƙashin Jam’iyyar APC
10• Hon. Nnabuife Chinwe Clara
Daga jihar Anambra a ƙarƙashin Jam’iyyar YPP
11• Hon. Lilian Obiageti Orogbu
Daga jihar Anambra a ƙarƙashin Jam’iyyar LP
12• Hon. Gwacham Maureen Chime
Daga jihar Anambra a ƙarƙashin Jam’iyyar APGA
13• Hon. Marie Enenimiete Ebibake
Daga jihar Bayelsa a ƙarƙashin Jam’iyyar PDP
14• Hon. Regina Akume
Daga jihar Benue a ƙarƙashin Jam’iyyar APC
15• Hon. Ibori-Suenu Erhiatake
Daga jihar Delta a ƙarƙashin Jam’iyyar PDP
16• Hon. Fatima Talba
Daga jihar Yobe a ƙarƙashin Jam’iyyar APC
17• Hon. Blessing Amadi
Daga jihar Rivers a ƙarƙashin Jam’iyar PDP
Don haka, Majalisar Wakilai a shekarar 2024 ta gabatar da wani ƙuduri a zauren Majalisar ta wanda ya buƙaci a Samar da ƙarin kujeru na musamman waɗanda Mata ne kawai za su yi takarar wannan kujerar. Ƙudurin ya buƙaci a gyara Sashi Na 48, 49 da Kuma 91 Na kundin tsarin Mulki.
Kundin dokar ya bayyana cewa: kowace Jiha za a ware mata kujerar Senator guda ɗaya da Kuma House of Rep. shima guda ɗaya, kunga Kenan tsakanin Majalisar Wakilai da ta Dattijai za a Samu Mata mutum Saba’in da huɗu kenan. Sannan Majalisun jihohi su ma kowace Jiha za ta ware kujera Uku waɗanda Mata ne Kawai za su yi takarar waɗannan kujerun hakan yake nuna za a iya samun Karin Mata mutum 108 a Majalisun jihohi, Idan muka haɗa lissafi zai zama an samu ƙarin ‘yan Majalisu Mata na dindindin da yawan su ya kai ɗari da tamanin da biyu. Sannan Kuma wannan dokar ba za ta hana Matan su yi takarar sauran kujerun Majalisun jihohi da na tarayya ba.
Wannan ƙudurin dokar yana gaban Majalisa, duk da dai an taɓa gabatar da shi a shekarar 2021 Amma Bai Samu tsallakewa ba shi ne aka sake gabatar da shi a shekarar 2024.
Bissalam
Shehu Rahinat Na’Allah
22nd February, 2025.
Leave a Reply