An dakarda Senator Natasha Akpoti Uduaghan daga majalisa har tsawon wata shidda.
Wato yau na kara koyar wani darasi gameda rayuwar duniya. A lokacinda Senator Akpabio yace wayanda ke goyon bayan a dakatarda senator Natasha suce “I”, sai naji duk house ya dauka “I,I,I…….”. Daga baya sai yace wayanda basa goyon bayan a dakatarda ita suce “nay”, sai naji shuru kamar anyi mutuwa.
Abin Lura:
1-Idan ka samu matsala da manyan mutane, toh kowa juya maka baya yake, harda abokan ka. Kai idan kaci rashin sa’a harda yanuwan ka na jini sai kaga sun juya maka baya sunce bakada kirki.
2- Idan kuka lura da yada abin ya kaya a majalisa yau, tabbas zaku lura da cewa harda masu zuga Senator Natasha sun juya maya baya.
3- A tawa fahimta, babban wurinda Natasha ta samu matsala shine yada ta shigo da batun “sexual harassment” dinnan. Tun a wancan lokacin, don me batayi magana ba sai a wannan qadamin? Abu ne mai yuwa ya faru ko bai faru ba, ni dai ban sani ba. Allahu a’alm.
4- Bana goyon bayan a janye mata jami’an tsaro, sa’annan kuma idan ta rubuta takarda bada hakuri kamar yada majalisa ta nema, toh ina goyon bayan a sassauta mata wa’adin izuwa wata 2-3.
5- Wato majalisar sun tsarata ne kan dokoki, kuma ga abinda ya bayyana, ta sabawa dokokin. Ina daga cikin wayanda suka yaba mata sosai a lokacinda tayi tsaye tsayin daka a majalisa akan cewa ba zata yarda a canza mata wurin zama ba kuma dolen-dole sai tayi magana. Ni har ga Allah a wancan lokacin ban sanda cewa abinda tayi ta sabawa dokar majalisa ne ba saida naji ana karanto dokokin sai nace Subhanallahi ashe na goyi bayan ta a bisa kuskure.
6- Daga karshe, ya kamata gwamnati ta sulhunta Akpabio da Natasha a bayan fage.
Leave a Reply