Tarihi: Cikakken Tarihin Lata Mangeshkar Yar India Da (Ta yi wakoki Dubu 25 da harsuna 36)

Tarihin Shahararrun Mata
Lata Mangeshkar (Ta yi wakoki Dubu 25 da harsuna 36)
Lata Mangeshkar Wanda Asalin Sunanta shi ne Hema Mangeshkar; mawaƙiyar Indiya ce Ana ganin ta a matsayin daya daga cikin manyan mawakan da suka fi tasiri a yankin Indiya. Muryar ta na ɗaya daga cikin abubuwan da ke haɗa kan mutanen Kudancin Asiya. Gudunmawar da ta bayar ga masana’antar kiɗa ta Indiya a cikin sana’ar da ta shafe shekaru 80 ta sami lakabi na girmamawa kamar “Sarauniyar Melody”, “Nightingale of India”, da “Voice of the Millennium.
Fitacciyar mawakiya kuma daya daga cikin mawakan da ake girmamawa a kasar India wato Lata Mangeshkar itace mawakiyar da ta ke waka a cikin harsuna 36 na kasar Indiya da ma na wasu kasashen waje.
An haifeta a ranar 28 ga watan Satumbar 1929, ta mutu dalilin cutar korona a ranar 6 ga watan Fabrairu 2022, ta na da shekaru 92 a duniya. 
Sunanta na ainihi Hema Hardikar Mangeshkar, kuma ita ce babba a wajen iyayenta inda ta ke da kanne uku. Tun tana shekara biyar da haihuwa ta fara fitowa a wasu wakoki na babanta, koda ya ke ba wakar ta ke ba a lokacin.
Tun tana karama ta ke da sha’awar waka, hakan ya bawa babanta damar karfafa mata gwiwa a kan abinda ta ke so. Tana da shekara 13 ne bayan rasuwar mahaifinta, aminin babanta ya dauki nauyinsu, har ma ya taimaka mata wajen cimma burinta na zama mawakiya.
Yaushe ta fara waka?
A 1942 ne Lata, ta fara waka, koda ya ke a lokacin mutane kan yi korafin cewa muryarta ta fiye sirinta, don haka ne ba a fiye bata waka ta yi ba. Amma duk da haka gwiwarta ba ta yi sanyi ba, a haka ta ci gaba da fadi tashin ganin ta samu damar yin waka a fina-finai. Wakarta ta farko ita ce wadda ta rera a 1943 a wani fim din Marathi mai taken Gajaabhaau.
A shekarar 1945 ne Lata, ta koma Mumbai da zama kasancewar can ne cibiyar fina-finai ta kasar India don cimma burinta. A nan ne abokin babanta ya rinka kai ta wajen masu shirya fina-finai domin ta yi musu waka, a haka dai tun suna kushe muryarta, har kuma suka gano cewa lallai tana da murya. Wakarta ta farko ta tayi fice a fina-finan Hindu, itace wadda ta yi a shekarar 1948 a fim din Majboor wato wakar “Dil Mera Toda, Mujhe Kahin Ka Na Chhora”.
Har karshen Rayuwarta Lata na alfahari da wannan wakar da kuma wanda ya sa ta yi masa wakar. Daga nan ne fa tauraruwar Lata ta waka ta fara haskakawa, saboda sai ta rinka yin wasu dabaru na sauya murya kala-kala idan tana waka.
Wannan salo na ta ke ba wa masu shirya fim da masu rubuta waka sha’awa, suke kuma rububinta a kan ta yi musu waka.
Da sannu a hankali har Lata ta ja hankalin kanwarta, wato Asha Bhosle a kan ita ma ta fara waka, kuma fara, mutane kuma suka yaba muryarta. Lata ta yi wakoki fiye da dubu 25 a harsuna daban-daban, haka kuma ta yi wakoki a fina-finai kamar na Hindi da Urdu da Tamil da Benghali da dai sauransu.
Tana jin yaruka da damam hakan ya bata dama ta yi wakoki a harsuna fiye da 36 ciki har da wanda ba na kasarta ba.
Lata, ta shafe shekara 70 ta na waka, kuma har ta kai shekara 60, muryarta ba ta canza ba, sai daga baya saboda shekaru.
Ko ta na da iyali?
Iyalan Lata sune ‘yan uwanta, domin bata taba yin aure ba, dalili kuwa shi ne saurayinta da suka yi soyayya wato Raj Singh Dungarpur iyayensa ba su amince da aurensu ba, gashi kuma su shaku sosai. Koda iyayensa suka hana shi auren Lata, sai ya ce tunda an hana shi abinda yafi so a duniya, to fa shi ya yi sallama da aure. Haka ya yi ta zama har ya mutu, itama kuma har ta mutu ba ta yi aure ba, kuma sun kasance suka mutu suna aminci da juna.
Shin Lata waka kawai ta ke yi?
Lata ba ta tsaya kadai a waka ba, domin ta kan rubuta wakar ma, kuma mai shirya wakar ce ma har ta bayar da shawara a kan kida da zai hau da wakar.
Tayi wakoki da suka yi fice da dama kamar wakar Ek Pyaar Ka Nagma Hai da Hum Dono Do Premi da Kanchi Re Kanchi Re da Ye Kahan Aa Gaye Hum da Sheesha Ho Ya Dil Ho da Tere Liye da Dil to pagal hai da Apne Pyar Ke Sapne Sach HueHum Aur Tum da Tu Mere Saamne da Sar Se Sarke da Tere Mere Honthon Pe da Kabhi Main Kahoon da Dekha Ek Khwab da Kabhi Kabhie da kuma Are Re Are.
Wadannan kadan ne daga cikin wakokin da Lata Mangeshkar ta rera.
Lata Mangeshkar ta samu lambobin yabo da dama ciki har da National Film Awards uku da Filmfare awards. A cikin 1989, Gwamnatin Indiya ta ba ta lambar yabo ta Dadasaheb Phalke. A cikin 2001, don jin daɗin gudummawar da ta bayar ga al’umma, an ba ta Bharat Ratna, ta zama mawaƙiya ta biyu kawai da ta sami babbar lambar yabo ta farar hula ta Indiya. A cikin 2007, Faransa ta ba ta lambar yabo ta Jami’ar National Order of the Legion of Honor, lambar yabo ta farar hula mafi girma a ƙasar.
An sanya ta a cikin littafin Guinness World Records a matsayin mai mafi yawan rubuce-rubucen waka a tarihi kafin a maye gurbinta da ‘yar uwarta, Asha Bhosle.

Published on: March 3, 2025. at: 9:41 pm

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*