Mako uku bayan gano tana ɗauke da cutar kansar bakin mahaifa, Sayar Devi Modi mai shekara 88 ta ƙi neman magani, a maimakon haka ta yanke shawarar yin azumi don ta mutu.
Gwajin da aka yi mata ranar 25 ga watan Yuni, ya nuna cewa cutar tata na yaɗuwa.
A ranar 13 ga watan Yulin 2024 ta buƙaci yin wanka. Kwana guda bayan haka ta kira mu ta sanar da mu aniyarta na fara santhara,” a cewar jikanta, Pranay Modi.
Santhara, wanda aka fi sani da sallekhana, wata ibada ce da mabiya addinin Jain, inda suke daina cin abinci da ruwan sha domin su mutu.
Ibadar ba ta cikin manyan ginshiƙan addinin. Kafofin yaɗa labaran Indiya sun yi ƙiyasin cewa ƙalilan ne daga cikin mabiya addinin Jain – wato 200 zuwa 500 ke mutuwa a kowace shekara sanadiyyar wannan ibada.
Wasu masu adawa da ibadar cikin mabiya addinin, na kiranta da ‘ƙunar baƙin wake’, inda buƙatar haramta Santhara ke gaban kotun ƙolin ƙasar Indiya.
Addinin Jain
Zaman lafiya na daga cikin manyan ginshiƙan koyarwar Jain, addinin da ya samo asali aƙalla shekara 2,500 da suka gabata.
Addinin bai yi imani da wani abun bauta ba, amma mabiya addinin sun yi imani da tsarkakken ruhi, madawwami kuma kaɗaitacce masanin komai.
Kusan duka mabiya addinin Jain ba sa cin nama, kuma sukan mayar da hankali wajen kyawawan halaye da gudun duniya.
Akwai mabiya addinin Jain kusan miliyan biyar a Indiya, kuma masu ilimin boko ne, domin kuwa wata cibiyar bincike ta Amurka na cewa kashi ɗaya cikin uku na matasa mabiya addinin na da digirin farko, idan aka kwatanta da kashi 9 cikin 100 na duka al’ummar Indiya.
Kuma da dama daga cikinsu na da arziki mai tarin yawa.
Al’ummar Indiya na girmama tare da martaba malaman addinin Jain.
Ko a baya-bayan nan ma Firaministan ƙasar, Narendra Modi ya wallafa wani saƙon alhini na mutuwar wani malamin addinin a shafinsa na X, inda ya bayyana mutuwar Acharya Shri Vidyasagar Ji Maharaj a matsayin ”rashin da ƙasar ba za ta iya maye gurbinsa ba”.
Malamin addinin – wanda ake girmamawa – ya mutu ne yana da shekara 77, bayan shafe kwanaki uku yana azumi, inda dubban mutane suka halarci jana’izarsa.
Mabiya addinin Jain sun ce wannan ibada ta mutuwa ta hanyar azumi ba za a haɗa ta da ”kisan rahma ko taimaka wa ƙunar baƙin wake ba”.
“Sallekhana ko santhara ya sha bamban da taimaka wa ƙunar baƙin wake, azumi ne, ba wani magani ake sha ba, ba allura ake yi ba da zai sa ka mutu,” kamar yadda Farfesa Steven M. Vose, ƙwararren masanin addinin Jain a Jami’ar Colorado-Denver, ya shaida wa BBC.
Farfesa ya ce wannan al’ada ta azumi don mutuwa a addinin ya samo asali tun ƙarni na shida.
Taron alhinin mutuwa
Imani da ‘karma’, ruhi da sake haifo ruhi su ne manyan ginshiƙan santhara.
Wasu mabiya addinin, irin su Sayar Devi sun zaɓi wannan hanyar mutuwa a lokacin da ta fahimci ta kamu da cutar ajali.
A cikin bidiyoyin da aka ɗauka a lokacin da take azumi, Sayar Devi na sanye da farin tufafi, inda ta rufe bakinta da wani tsumma.
“Tana cikin nutsuwa, da hayyacinta kuma tana magana har numfashinta na ƙarshe,” a cewar Pranay Modi ɗaya daga cikin danginta.
Modi ya ce a lokacin azumin ƙarshe na kakar tasa, gidansu da ke Kabridhma a tsakiyar Indiya ya cika da jama’a tamkar ana biki.
“Gidan bai yi kama da na mutuwa ba, ƴan’uwa da dangi da abokai da makwabta, da matafiya da dama sun shigo gidan domin neman tabarrukinta.”
A kwanakin ƙarshe na azumin nata, Devi ta samu ƙarfin gudanar da ibadar Jain ta tsawon mintuna 48.
“Na tabbata za ta ji zafin ciwon sosai bayan daina shan magungunanta, amma ba ta yi wani ƙorafi kan hakan ba, ta kasance cikin kwanciyar hankali da nutsuwa har lokacin da rai ya yi halinsa,” cewar Modi.
Devi ta cika a gaban ƴaƴa da jikoki da tabbata ƙunnenta.
“Ban ji daɗin kasancewa a gabanta lokacin da take cikawa ba,” in ji Modi, “amma na san za ta samu makoma mai kyau. Mun girmama zaɓinta.”
Abu na ƙarshe
Ba koyaushe Santhara ke zama kyakkyawar cikawa ba, a cewar Farfesa Miki Chase da ta yi rubutun digirinta na uku kan wannan batu, kuma ta shaida gomman cikawa irin wannan.
“Wani mutum da ya kamu da cutar ajali ya yanke shawarar yin azumin mutuwa (santhara), kuma ya kasance cikin tsananin jin zafi, kodayake danginsa sun yi alfahari da hakan, kuma suka tallafa masa, amma ba su ji daɗin ganinsa yana shan wahala ba,” in ji Farfesa Chase, wanda a yanzu shi ne shugaban sashen nazarin addinin Jain a Jami’ar Wisconsin-Madison.
A wani batun na daban kuma, Chase ya ga wata mata da ta kamu da cutar kansa, kuma ta ajali, wadda ta samu nutsuwa bayan fara azumin.
“Surukarta ta shaida min cewa suna ganin hakkinsu ne a matsayinsu na iyali su ƙarfafa mata gwiwa da kuma tabbatar da ƙudurinta, don haka za su riƙa rera mata waƙoƙin bege.”
Farfesa Vose ya yi imanin cewa babu makawa ana shan wahala kafin mutuwar.
“Ba abu ne mai daɗi ka kalli mutum yana mutuwa saboda yunwa ba, kuma lokacin na iya zama abin ban tsoro. Mutum zai iya neman abinci ko ruwa yayin da jiki ke kokawar fitar rai, wanda ba za a ba shi ba, amma ana gane wannan a matsayin wani ɓangare na ƙarshe,” in ji shi.
An yi imanin cewa mata ne mafi yawan waɗanda suka fi zaɓar ‘santhara’. Farfesa Vose ya yi imanin cewa hakan ya faru ne saboda yadda ake ganin mata a matsayin masu tsoron Allah, da kuma yadda suke iya fin ƙarfin maza.
Farfesa Chase ya ce al’umma na kallon santhara a matsayin “babban nasara a fitar ruhi”.
Imani da ibadar
Shri Prakash Chand Maharaj Ji (da aka haifa a 1929) ɗaya ne daga cikin manyan sufayen Jain na ɗariƙar Svetambara – masu sanya fararen tufafi.
Ya shiga rayuwar zuhudu a shekara ta 1945. Mahaifinsa da kanensa suma sufaye ne kuma sun yi azumin mutuwa ‘santhara’.
“Ban damu da ganin mahaifina da ƙanina ba, gaba ɗaya na rabu da su, ban ji an mayar da ni maraya ba ko za a sami giɓi a rayuwata ba.”
Malamin addinin mai shekara 95 na zaune ne a wani gidan ibada a garin Gohana da ke arewacin Indiya. Ba ya amfani da wayoyi ko kwamfuta kuma ya yi magana da BBC ta hannun almajirinsa, Ashish Jain.
“Kyakkyawar mutuwa a matsayin cikakkiyar ƙarshen rayuwa da kyakkyawar mafarin gaba ta dogara ne akan ƙa’idodin falsafa na, na ruhi a addini,” kamar yadda ya shaida wa BBC.
Malamin ya ce santhara ya ƙunshi matakai da yawa, kuma ba zai iya zama kwatsam ko kuma abin sha’awa ba. Mutum yana buƙatar izini daga dangi da jagora daga malaman ruhi kamar Maharaj Ji.
Matakin farko na santhara shi ne tunani da kuma yarda da duk zunubai da ayyukanku na baya, sannan sai a nemi buƙatar gafara.
“Ta hanyar azumi domin mutuwa mutum zai iya wanke jiki da rai da kuma goge zunubi don rayuwa mai kyau ta ruhi a cikin haihuwa mai zuwa,” Maharaj Ji ya bayyana.
“A ƙarshe zai ƙare a cikin ‘yantar da rai daga sake haihuwa da mutuwa.”
Ɗaukar matakin shari’a
A shekarar 2015, wata babbar kotu a jihar Rajasthan da ke arewa maso yammacin Indiya ta haramta wannan ɗabi’a, amma daga baya kotun kolin ƙasar ta dakatar da hukuncin.
Tsohon ma’aikacin gwamnati D.R Mehta na ɗaya daga cikin masu shigar da ƙara da ke son kiyaye al’adar santhara.
“Mabiya addinin Jain suna ganin wannan a matsayin mafi kyawun nau’in mutuwa. Mutuwa ce ta hankali da lumana da mutunta yarda da mutuwa. tsarkakewa ta ruhi da kuma zaman lafiya na har abada su ne manyan dalilai, “in ji Mehta, wanda ya riƙe mukamai kamar mataimakin shugaban babban bankin Indiya da shugaban hukumar kula da kasuwannin hannayen jari.
Adawa da wannan al’ada dai ya sake kunno kai sakamakon mutuwar wata yarinya mai shekara 13 daga Hyderabad a shekarar 2016.
Ta rasu bayan ta yi azumin kwanaki 68, amma duk sauran ‘yan Santhara a ‘yan shekarun nan tsofaffi ne.
Leave a Reply